25/02/2026
Shi fa wannan yaron namu na FMK, ɗan shekara 6, ba ruwansa da yin azumi, amma idan lokacin sahur ya yi, dole yana gaba-gaba.
Idan lokacin buɗa baki ya yi ma, shi ne a gaba!
Abin mamaki ma, idan ana haɗa kayan buɗa baki, har cikin sassanyar murya ake tambayarsa:
“Bilal, me za ka ci a cikin kayan nan?”
Sai ya ɗauki kusan minti goma yana tunani kafin ya ce ma Inna tai ta ƙara masa wani abu a gefe.
Da zarar ya ɗan ci wani guntun abu daga cikin kayan turawa, sai kuma a sake tambayarsa:
“Bilal, ya ka ji? Yayi daɗi?”
Kai! Kamar dai shi ne mai gidan gabadaya 😄
Amma fa, mu ‘ya’yan Malam Shehu irinmu, ka isa a ce za a yi sahur ka tashi amma ba azumi za ka yi ba? Wa ya riƙa maka? In ka kuskura ka ci abincin sahur ba tare da niyyar azumi ba, wallahi da rana ba za ka sake ganin komai ba!
Ballantana ma lokacin buɗa baki, kowa ya gaji da yunwa, ana shirin shan ruwa, sai a ce ana zuba maka kunu kaɗai ka fara sha kafin kowa… Kai, sai dai ka yi addu’ar zaman lafiya! 😄
Bilal dai, ka ci gaba da tashi sahur, a yi buɗa baki da kai, kana cikin alkhairi dumu-dumu.